1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yaki da Boko Haram da sauran gyara

November 14, 2017

Talakawan da ke rayuwa a wasu sassan jihar Borno, sun aza ayar tambaya kan aikin yaki da harkokin mayakan Boko Haram, suna mai cewa batun sauki a lamarin bai shafi yankunan da suke ciki ba.

https://p.dw.com/p/2ncbh
Nigeria Militär Präsident Muhammadu Buhari
Shugaba Buhari da hafofoshin tsaro a SambisaHoto: NPR

Al'umomin da ke zaune a wasu yankunan kudanci da arewacin jihar Borno sun ce sun fara dawowa daga rakiyar ikirarin da gwamnati da jami'an tsaron Najeriya ke yi dangane da yaki da Boko Haram saboda yadda ake kai hare-hare a kauyukansu tare da kona musu gidaje da kwashe musu kayan abinci. Kusan a kullum mayakan Boko Haram na kai hare-hare ne ga kayukan daban-daban a sassan arewaci da kudancin jihar Borno da kuma wasu sassan jihar Yobe inda ake da karancin jami'an tsaro ko kuma kauyukan na nesa daga inda aka girke jami'an tsaron. 

Nigeria Kano Selbstmordanschlag
Hari a wata kasuwaHoto: picture-alliance/dpa/Str

Mayakan na Boko Haram na tsananta kai hare-hare a yankunan Damboa da ma garuruwan da ke kusa da birnin Maiduguri, kamar Molai da kuma wasu kauyuka a arewacin jihar Borno. A jihar Yobe mai makobtaka da jihar ta Borno, mayakan na zafafa kai hare-hare a yankuna Gujba da Gulani da kuma Sasawa. 

Ko a baya bayan nan ma, mayakan Boko Haram sun shiga garin Muktum da ke yankin karamar hukumar Gujba suka hallaka wani da aka ce mahaifi na ga daya daga cikin mayakan kungiyar. Wannan ya sa wasu mazauna kauyukan suka fara tserewa daga garuruwansu saboda matsin lamba na hare-haren mayakan Boko Haram wanda kusan kullum suke afka musu tare da kwashe musu kayayyaki da ababen hawa.

A cewar galibin mutane a kauyukan da ke zaune a jihar ta Borno, mayakan Boko Haram na nan jibge a wuraren da ba su da nisa da garuruwansu. Masana dai sun bayyana bukatar mutane a nasu bangaren, su bada ta su gudumowar wajen sanar da jami'an tsaro halin da su ke ciki inda kuma su ka jinjinawa jami'an tsaro saboda yadda suka samar da zaman lafiya a yankuna da dama kuma a cewar yakin sukuru ba a kare shi lokaci guda.