1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Takaddama kan sauya taken kasa

May 30, 2024

Kasa da sa'oi 24 da sake kaddamar da tsohon taken Najeriya, takkadama ta barke cikin kasar inda ra'ayi yake rabe a tsakanin masu tunanin taken ya hau hanya da masu fadin bashi da tasiri

https://p.dw.com/p/4gTEr
Nigeria Einweihung des neuen Präsidenten Bola Ahmed Tinubu
Hoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

A cikin sabon fata na sake cusa son kasa a zukatan miliyoyin al'umma Najeriya ta sauya zuwa ga sabon taken kasa..

To sai dai kuma tun ba‘a kai ga ko'ina ba taken na shirin komawa wani abun da ke kama da wasan yara, a zuciyar yan kasar da hankalinsu ke kara karkata zuwa tsaro da abinci

Tuni dai aka baiwa wasu jami'an gwamnatin kasa da kwanaki hudu na haddace sabon taken a cikin fatan sake kaishi tudu da gangare cikin kasar da yan mulkinta ke fadin da sauran gyara.

Ya zuwa yanzun dai hankali na masu mulkin na kara karkata zuwa batun ilimantarwa bisa dokar da kasar ta gada daga yan mulkin mallaka, kafin rusa ta a shekarar 1978.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Ubale Musa/DW

Hon Alhassan Rurum na zaman dan majalisar wakilan kasar, daya kuma cikin masu taka rawa zuwa ga sabuwar dokar da ke jawo kace nace a halin yanzu.

Koma ya zuwa ina ake shirin a kai da nufin sauya tunanin da kila kai da'ar ma zuwa zukatan al'umma, tuni dai dokar da ke da tarihi irin na mulkin mallaka ke jawo takaddama cikin kasar ahalin yanzu.

Dr Faruk BB Faruk mai sharhi kan siyasa kasar yace sabon taken na da kokarin mai da kasar baya.

Majalisar dokokin Najeriya
Majalisar dokokin NajeriyaHoto: Nigeria Office of the House of Representatives

Sake cusa tunani irin na turawan mulkin mallaka tuni wasu kalmomin da ke cikin sabon taken suka bace har a cikin kamus irin na turawan yamman, Haka kuma ita kanta dokar da ta tabbatar da sabon taken, bata cika ka'idar yin doka a cikin zauren majalisu ba , a fadar Farfesa Mustapha Osuji dake zaman kwarrare bisa dokokin kasar.

Tuni dai wasu jiga jigan yan kasar suka nuna bara'a bisa taken da suke fadin bai yi dai dai da tunaninsu ba, cikin kasar da hankali yake ta karkata bisa batu na rayuwa cikin halin matsatsi.

Kuma ko bayan nan an kaddamar da sabon taken a lokacin da daukacin yankin kudu maso gabashin kasar ke kulle, bisa umarnin IPOB da ke juyayin yakin basasa na kasar yau din nan.

Abun jira a gani dai na zaman dabarar iya kaiwa ga sake kishin kasa, a tarayyar Najeriya da kai yake rabe bisa batun kabila da kila ma hanyoyin kaiwa ya zuwa fin karfin batun tsaron da abinci.