Najeriya: Tsaro ya dawo a gabar tekun Guinea
October 6, 2022Daga shekarar 2017 zuwa 2020 dai an sace sama da ma'aikatan jirage na ruwa 140 a wasu jerin hare-hare sama da 400 a ruwayen kasar da makwabtanta. A shekarun baya dai, kama daga satar danyen mai ya zuwa fashin jirage na ruwa a daukacin gabar ruwayen Guinea da ta kunshi kasashe guda shida dai na zaman ruwaye mafi hatsari a duniya baki daya. Sai dai a yanzu a sakamakon sabon shirin samar da tsaro kasar ta ce ta samu saukin matsalolin. Shirin kuma da kasar tace na tasiri wajen tabbatar da tsaro cikin ruwaye na kasar.
Cikin sama da shekara guda da kaddamar da shirin na Deap Blue dai babu ko da jirgi guda daya da ya fuskanci hari a fadar hukumar kula da tsaro da gudanarwar ruwayen kasar ta NIMASA.
Shugaban hukumar Bashir Jamoh dai ya ce Najeriyar na ganin ingantacce na ci gaba a ruwaye na kasar da ke da tsawon kilomita sama da 800 kuma mafi dauka na hankali a duniya baki daya.
Sama da kaso 70 cikin 100 na hada-hadar jirage na ruwa a kasashen gabar ta Guinea dai na gudana ne a cikin Najeriya, kasar kuma da ke ji a jika daga satar danyen man da ke zaman abun alfaharin mahukuntanta.
Kabiru Adamu masani da ke sharhi bisa batun tsaro ya ce samun zaman lumana a tekun na da alaka da sauyi na sana'a ta barayin da suka koma satar danyen mai maimakon hari bisa jiragen na ruwa.