Najeriya ta samu koma baya a sha'anin mulki
October 24, 2024Wani sabon rahoton shugabanci a nahiyar Africa ya ce tarayyar Najeriyar ta zama baya ga dangi kan sha'anin mulki a tsakanin al'umma.
Rahoton Mo Ibrahim da ya yi nazarin mulkin a tsakanin kasashen Afirka 54 ya ce, Najeriyar ta gaza a fannoni daban daban cikin harkar mulkin.
Kasar dai ta koma ta 11 cikin mafi lalacewa a nahiyar sakamakon rashin tsaro da tattalin arziki a shekaru 10 da suka gabata.
Rahoton ya kuma ce Najeriyar ta gaza yakar cin hanci da rashawa, sannan kuma ta gaza tabbatar da yancin a wataya ta fannonni daban daban.
Rahoton dai na kara fitowa fili da yadda tsarin demokaradiyya ke neman gaza kai wa ga biyan bukatun miliyoyi cikin kasar dake da babban fata kansa.
Isa Yuguda tsohon gwamnan jihar Bauchi da kuma ya ce abun da ke akwai a tarayyar Najeriya na da ruwa da tsaki da gazawa ta tsohuwar gwamnatin kasar.
Kokari na komawa tushe ko kuma neman rushe lamura dai, kusan daukacin shekarun 10 da suka gabata sun faru ne a karkashin masu tsintsiyar tarayyar Najeriyar.
Akwai dai zargin APC da ta karbi mulki a shekara ta 2015 a cikin alkawarin gyara kurakuran PDP ta kare da kara rusa daukacin ginshikin harkokin mulkin.
To sai dai kuma abun da ke faruwa a shekarun APC a tunanin Abdullahi Umar Ganduje shugaban jam'iyyar APC mai mulkin kasar, na kama da kokarin daukar saiti cikin kasar da ke tangal tangal.
Fatan sauyi zuwa gaba, koma nisa a cikin rudani dai, tarayyar Najeriyar ta dade tana karatun sauyin amma kuma tana kara ganin sauyi irin na mai haka rijiya.
Farfesa Attahiru Jega kwarrare ne a harkar mulki da siyasa, kuma ya ce mayar da siyasar zuwa sana'a ne ya kai kasar cikin rudun da ke da girman gaskiye.
Najeriyar dai ta bi sahu cikin lalacewar da kasashe irin su Niger, da Burkina Faso da Mali da ke karkashin mulkin soja suka yi.