1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Gwamnatin Najeriya ta ce ta samar da abinci ga yara

June 26, 2024

Yayin da ake ci gaba da fuskantar mummunan karanci na abinci tsakanin yara 'yan kasa da shekaru biyar gwamnatin Najeriya ta ce ta samar da abinci ga yara miliyan da doriya da ke fuskantar tamowa a sashen arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4hXHA
Najeriya
Yara na fuskantar karancin abinci a NajeriyaHoto: ASSOCIATED PRESS/picture alliance

Tun daga farko na watan nan ne dai dama kungiyar likitocin nagari na kowa suka koka bisa karuwar ta yaran dake da bukatar abincin gaggawa a cikin neman kai karshen annobar tamowa dake kara yaduwa a sashen arewacin kasar a halin yanzu. Daukaci na cibiyoyi na kungiyar 50 dai sun cika makil da yaran dake cikin tsananin yunwa sakamakon rashin isashe na abinci.

Karin Bayani: Najeriya: Kokarin shawo kan matsalar karancin abinci

Najeriya | Sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno
Yara na fuskantar karancin abinci a NajeriyaHoto: Adam Abu-bashal/AA/picture alliance

Kungiyar dai ta ce kididdiga ta yawan yaran da kann fuskanci irin wannan matsala ya karu da kusan kashi 100 cikin 100 a cibiyoyin karban abincin. A cikin wannan mako dai an rika nuna hotunan wasu yaran da kasusuwansu ke waje sakamakon annobar rashin isasshen abinci a wani abin da ya tada hankalin da dama a sashen arewacin Najeriya. Ita dai Najeriya tana zaman kasa ta biyu mafi yawan yaran da ke da karancin abinci a duniya baki daya.

To sai dai kuma a fadar Farfesa Mohammed Ali Pate da ke zaman ministan lafiya da inganta rayuwar al'umma a kasar dai, Najeriya tana daukar jerin matakan fuskantar matsalar da ke dada kamari a daukacin sassan arewa a yanzu haka. Za a ba mata miliyan daya da dubu dari uku, musamman masu juna biyu domin taimaka sake habbaka musu tsarin jikinsu.

Yara sama da miliyan daya da Dari Uku ne dai ke fuskantar tamowar cikin arewacin kasar da ke zaman tungar rigingimun rashin tsaro, kuma hedikwata ta talauci ta kasar. Kimanin kashi 32 cikin 100 na yaran na arewa dai na fuskantar tawaya sakamakon rashin abincin da ke ginin jiki. Kafin matsalolin rashin tsaro da hauhawa ta farashi su kara jawo rikicin da ke zaman barazana mai girma cikin kasar a halin yanzu. Wata sanarwar hukumar kula da yara ta majalisar dinkin duniya dai ta ce Najeriya tana da bukatar tsabar kudin da ya kai dalar Amurka miliyan 306 da nufin tunkarar karancin abinci a sashen arewa maso gabashin kasar kadai.