Najeriya: Shari'ar Diezani Alison-Madueke
April 6, 2017Wannan zargi da ake wa tsohuwar ministar kula da harkokin mai ta Najeriya Nigeria Diezani Alison-Madueke a gaban kotu da ma yadda daya daga cikin ma'aikatan hukumar zabe ya amsa cewa lallai ta bashi cin hanci na Naira milyan 30 kuma ya karba babban lamari ne a tuhume-tuhume da hukumar yaki da halasta kudaden haram ta EFCC ke gabatarwa a kan wannan batu.
Baya ga batu na bada cin hanci ga ma'aikatan hukumar zaben Najeriya din don sauya alkaluman zabe na shakrar 2015, har wa yau kotu na zargin tsohuwar ministar da karkatar da kudi Naira biliyan 23 wanda ya kasance daya daga cikin zarge-zarge na nuna halin bera da akewa tsofaffin jami'an gwamnati.
Zargin rub da ciki kan dukiyar kasa da har yanzu ake ci gaba da bankadowa tamkar almara ya sanya masharhanta da 'yan kungiyoyi na fararen hula da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriyar bayyana takaicinsa bisa ga irin koma-bayan da irin wannan ta'ada ke haifarawa musamman ga kasashe masu tasowa.
Yayin da kotu ke tuhumar ita wannan tsohuwar minista da kuma irin fadi-tashin da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ke cigaba da yi na bankado masu halin bera don gurfanar da su gaban shari'a a share guda kotu ta wanke alkalin wata babbar kotu a kasar wato mai shari'a Adeniyi Ademola daga duk wani laifi bayan da aka ambato sunansa cikin wanda ake zargi da karbar na goro.