Najeriya: Sabbin shugabannin majalisa ta goma
June 13, 2023Talla
A majalisar datawa Sanata Godswill Akpabio ne ya samu nasarar lashe zaben zama shugaban majalisar inda ya kayar da abokin takarasa Abdul'Azizi Yari. Nan take kuma aka rantsar da shi. Sanata Ali Ndume na cikin wadanda suka goyi bayan zaben Sanata Akpabio.
Ko yaya sauran ‘yan majalisa musamman na jamiyyar PDP ta ‘yan adawa suka ji da faduwa zaben da suka yi da ma kalubalen da ke gabansu?
A majalisar wakilan Najeriyar ma dai zaben aka yi inda suka yi amfani da salon ‘yar tinke.
Bayan kidaya kuru'un Hon Tajudeen Abbas wanda shine zabin jamiyyar APC shine ya zama shugaban majalisar wakilan ta 10.
Mata 15 ne kacal suka samu shiga majalisa ta 10 abinda ya nuna koma baya na shigar mata siyasa.