Mutum 49 sun mutu a sanadiyar ambaliyar ruwa a Najeriya
July 16, 2018Talla
Ruwan sama kamar da bakin kwarya daga daren ranar Lahadi ya zuwa Litinin ne ya janyo tunbatsar madatsar ruwan Tiga dam, wanda ya haifar da munmunar ambaliya a kauyukan da ke karamar hukumar ta Jibiya.
Amin Waziri shi ne sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa a jahar, ya tabbatar da faruwa lamarin da kuma kokarin da gwamnati ke yi na isar da taimako ga mabukata. Wasu kafafen yada labarai a jahar sun ce gidaje fiye da casa'in ne suka salwanta a sanadiyar iftala'in, baya ga asarar dabbobi sama da dari biyu da sittin. A na ci gaba da neman wasu mutanen da iyalansu ba su ji duriyarsu ba tun faruwar lamarin.