Najeriya: PDP ta yi barazanar kauracewa zabe a Bauchi
March 22, 2019Tuni dai jam’iyyar ta PDP ta bayyana cewa za ta garzaya kotu domin neman ayi mata adalci inda ta kafa hujja da kalaman da jam’iyyar APC ta yi cewa wani abu zai iya kasancewa idan aka sake zaben a kananan hukumomin jihar goma sha biyar wadanda ke da masu rajistar katin zabe da yawansu ya haura dubu ashirin da biyu. Dan takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar ta Bauchi.Sanata Bala Muhammad Kauran Bauchi yace bai kamata a gudanar da zaben cike gurbi ba har sai an kammala zaben da aka fara.
Sai dai a nasa bangaren shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi Uba Ahmad Nana yace idan jam’iyyar PDP ta na da kwarin gwiwar samun nasara babu abinda zai sa ta yi kasa gwiwa.
Jama’a da dama musamman magoya bayan manyan jam’iyyun biyu na cigaba da bayyana ra’ayoyin su dangane da karashen zaben da za’a gudanar a wannan asabar. Yanzu dai hankalin jama’ar jihar Bauchi ya karkata ne zuwa ga yadda zaben zai kasance domin sanin inda aka dosa da kuma jiran hukuncin da kotun tarayya a Abuja za ta yanke a ranar 23 ga wannan watan na Maris.