1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Oteh ta kama aiki a Bankin Duniya

Uwaisu Abubacar Idriss/GATSeptember 28, 2015

Orunma Oteh tsohuwar Shugabar Hukumar Kula da Hannayen Jari ta Najeriya ta kama aiki a wannan Litanin a matsayin mataimakiyar shugaban Bankin Duniya kuma akawun bankin

https://p.dw.com/p/1Gez9
Weltbank
Hoto: AP

A wannan Litanin ce tsohuwar Shugabar Hukumar Kula da Hannayen Jari ta Najeriya, Arunma Oteh ta kama aiki a matsayin mataimakiyar shugaban Bankin Duniya kuma akawun bankin, abinda ya kara daga matsayinta daga aikin da ta yi a Najeriya.

Arunma Oteh dai na daya daga cikin fitattun ‘yan boko daga Najeriyar da ke da ilimi mai zurfi a tun daga digiri na farko a fanin komfuta, ya zuwa jami’ar Harvard ta Amirka inda ta kware a fannonin cinikaiyya da tattalin arziki. Ta yi aiki a sassa daban-daban a Najeriyar da ma kasashen duniya, har da Bankin Raya Kasashen Afrika wato ADB. Shin wacece Arunma Oteh ne? Dr Obadiah Mailafia ya taba aiki tare da ita a lokacin da ta rike mukamin akwau a bakin raya kasashen Afrika.

Jim Yong Kim Präsident Welt Bank
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Seth Wenig

‘’Mace ce ta kwarai mai aiki da zurfin tunani, sai dai wani lokaci akwai yarinta kankani kadan a kanta, lokacin da ta zo aiki a Najeriya ba ta gane yadda za ta yi tafiya da manya ba, wato 'yan siyasa da sauransu. Amma tunda Bankin Duniya sun ga ta iya aiki suka bata to ya nuna muna da kwararru a Najweriya kenan. Amma dai ina fatan sabani da ya faru a lokacin da ta yi aiki bai kamata ta bari ya sake faruwa a can ba’’

Miss Oteh dai ta fuskanci korafe-korafe a lokacin da ta jagoranci hukumar kula da hanayen jari ta Najeriya, abin da ya sanya kai ruwa rana tsakaninta da ‘yan majalisar wakilan kasar,abin da ya yi dalilin gaza samun sabon wa’adi.To sai dai duk da wannan Shugaban Bankin Duniya Jim Young Kim ya bata wannan mukami inda zata jagoranci kulawa da makudan kudin bankin har dala bilyan150. Shin wani tasirin ilimin da ta ke da zai yi cikin tafiyar da aiki? Alhaji Shuaibu Idris Mikati masanin tattalin arziki ne a Najeriya.

Karte Nigeria Yobe Damaturu Deutsch/Englisch

"Maganar gaskiya it ace a ilimi na boko tana da ilimi don ta je makaramntun boko da kusan duk dan Adam yake da sha’awar ya je, amma karatu daban iya aiki daban, In ka zo wajen aiki wadanda duk suka zauna da ita a bakunan da ta yi aiki daga Center Point Merchant Bank har zuwa Bankin Raya Kasashen Afrika za ka ji sun ce akwai abubuwan da ya kamata a ce ta yi ba ta yi ba. Kuma ai hannu daya ba ya daukan daki".

Ga masu hada-hadar hanayen jari a Najeriya na cikin wadanda suka yi aiki da Arunma Oteh abinda ya sanya tambayar Malam Abubakar Aliyu me zai ce ga yadda ake kalonta.

"Samun mukaminta bai zo mana da mamaki ba, saboda mun san yadda aka yi ta zo Najeriya a hakumar da ke kula da hannayen jari, kuma mun san matsayin Bankin Duniya ga Afrika, ba damuwa ne ta yi ba ga ci gaban Afrika.Ga shi kuma mun gani ya nuna ga irin aiyukan da ita Oteh ta yi a nan Najeriya"

A yayinda ra’ayoyi suka sha bamban a kan sabuwar mataimakiyar shugaban bankin duniya kuma akawun bakin, za’a sa ido a ga manufofin da ta ce za ta maida hankali da suka hada da ci gaba da karfa Bakin Duniya a matsayin mai bada bashi bisa tsimi da alkinta hatsarin yin hakan.