1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Najeriya: Naira ta sake komawa cikin mawuyacin hali

May 8, 2024

Kasa da makonni uku da taka rawa mafi inganci a fannin kudi a duniya, darajar takardar kudin Naira ta sake faduwa kasa warwas, inda ake sayan kowanne Dalar Amirka daya a kan 1415 na Naira a halin yanzu.

https://p.dw.com/p/4fdmk
Ana canjin Dalar Amurka daya a kan Naira 1415 na Najeriya a yanzu
Ana canjin Dalar Amurka daya a kan Naira 1415 na Najeriya a yanzuHoto: Getty Images

A cikin kibtawa ta bisimillah ne Naira ta tarayyar Najeriya ta rikide daga kudi mafi taka rawa mai kyau a duniya ya zuwa ta kan gaba a fannin lalacewa. Rushewar kudin kasar daga kasa da Naira 1000 makonni uku baya ya zuwa Naira 1416 kan kowace Dala dai, ya tada hankalin 'yan mulkin tarayyar Najeriya da ke ta tsallen murnan kai karshen rikicin na kudi. Abin da ya kai hukumar EFCC da aiwatar da wani samame zuwa ga kasuwar 'yan canji da ke a Abuja.

Karin bayani: Najeriya na kokarin ceto darajar Naira

Akalla masu canjin biyu ne aka kame bayan daruruwan miliyoyi da jami'ai na hukumar EFCC suka kwashe bayan harbi da bindiga. Abdullahi Abubakar Daura da ke zaman shugaba na kungiyar 'yan canjin ta Abuja ya ce lamura sun koma dai ai bayan samamen da ya kai ga tada hankali na matasan 'yan canji.

Zentralbank von Nigeria

A baya, babban bankin kasar na CBN ya dauki jerin matakai da nufin sake farfado da darajar Naira da nufin kawo karshen hauhawar farashin da  tsadar kudaden kasashen waje da ke zaman barazana mai girma  a ckin kasar. Duk da cewar a takarda, bankin ya bayyana tsoma baki tare da fitar da darururwan miliyoyi na daloli da nufin tallafa wa Nairar, amma ga dukkan alamu akwai sauran tafiya a tsakanin kasar Najeriya da kaiwa ya zuwa sauke farashin.

Karin bayani: Samame a kasuwannin 'yan canji na Najeriya

Ana Kallon kokari na karfin hatsi a matsayin alamu na gazawar mahukuntan Abuja da ke tunanin mafitar a cikin halin  rudu. Umar Garkuwa ya share lokaci yana sana'ar canjin, kuma ya ce da kamar wuye batun murde wuyar 'yan canjin ya kai ga sake dora Nairar bisa hanyar girma. Tun ma kafin far wa masu takama a sana'ar canjin dai, an yi nisa a kace-nace tsakanin mahukuntan kasar da kamfanonin da ke hada-hadar kudi na fasaha ta zamani.

Binance-Kryptowährungsbörse Logo auf Smartphone und Bildschirm
Hoto: Silas Stein/dpa/picture alliance

Kamfanin Binance da ke cikin harkar kudin ya zargi jami'ain na Abuja da neman cin hancin Dala miliyan 150 da nufin sakin wani jami'i na kamfanin da ke hannun mahukunta tun kusan watanni ukun da suka gabata, zargin da masu mulki na kasar suke fadin ya saba wa hankali.

Ya zuwa tsakiyar Afirilun 2024, matakan Abuja sun yi nasarar mai da  Nairar zama kudi mafi taka rawa a duniya, bayan saukar ta daga kusan Naira 2000 a karshen watan Maris ya zuwa kasa da 1000. Abubakar Ali da ke sharhi a fannin tattali na arzikin tarayyar Najeriya ya ce tashin Naira tun daga farkon fari bai yi daidai da tattalin arzikin da ke cikin kasar a halin yanzu ba.

Karin bayani: Darajar Naira za ta ja baya a 2024 - Bloomberg

Sama da dalar Amurka miliyan 2000 ne dai bankin CBN ya batar a tsawon wata guda a yunkurin neman daga darajar kudin Naira, kuma  kawo zuwa dai kwalliya ba ta biyan kudin sabulu.