1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na neman bashin dala biliyan guda

February 10, 2017

Gwamnatin Nigeriya na neman bashin akalla dala biliyan 1 daga bankin duniya a yunkurin ta na fidda kasar daga matsin tattalin arzikin da ta ke fama da shi.

https://p.dw.com/p/2XKi5
Nigeria Abuja Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Krumm

Ya zuwa yanzu dai Najeriya ta shirya tsaf don gabatar wa bankin ka'idojin da ya ke bukata na tanadin da ta yi na matakan magance karyewar tattalin arzikin a karshen watan nan na Fabrairun da muke ciki, kamar yadda wakilai da kuma jami'an diplomasiyyar kasar suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Kasar da ke da arzikin mai, ta dai fara tsintar kanta a yanayin koma bayan tattalin arziki tun shekara ta 2014, har yanzu dai ta na cigaba da wata tattaunawa da masu bada lamunin da ke Washington tun shekarar da ta gabata a kan ta samu bashi don cike gibin kasafin kudin ta da kuma sauran ayyuka.

Har yanzu babu wani bayani a kan lokacin da Najeriya za ta mika wa masu bada lamunin matakan da ta dauka na magance karyewar tattalin arzikin duk kuwa da sanin kasar cewa bankin ba zai aminta da ba Nijeriya bashin da ta ke bukata ba har sai ta gabatar da wadannan ka'idoji.