1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matashi a NAjeriya ya kirkiro injin walda

October 9, 2019

A jihar Katsina da ke Najeriya wani matashi ya kirkiro injin walda wanda ke amfani da ruwa da wani sinadari yana ba da wutar lantarki dan saukakawa masu sana'ar walda.

https://p.dw.com/p/3Qyvy
Flash-Galerie Art Entreprise
Hoto: Chris Spatschek

Muhsun Aliyu Faskari shine matashin daya kirkiro wannan injin walda ya shaidama DW cewa kusan da manufa biyu rak ya kirkiro injin.

Wannan injin walda da na kirkira na kirkiroshi ne dan in zama mai dogaro da kai da kuma taimakon al'umma su zamo suna dogaro da kansu. Inji ne wanda za a iya a yi shi cikin sauki ba tare da ansha wahala ba cikin minti biyar sai a hada shi kuma inji ne wanda zai kawoma mutane saukin rayuwa dan tafiyar lamuran masu walda a sana'arsu

To ko menene banbancin wannan injin da matashi Musin ya kirkira da wanda masu walda ke amfani dashi a baya musamman bangaren farashi? Banbancin wannan da wanda suke amfani da shi a baya shi ne wancan za ka iya sayen shi dubu hamsun, dari abin da yai sama ya dai danganta da girman shi wannan kuma za ka iya sayen shi dubu biyu sannan wancan idan kai aiki da yawa dole zai dau zafi sai ka jira ya huta wannan kuwa za ka iya yin kwana uku har sati guda ba tare da ya yi zafi ba.

Akwai matasa da dama masu fasaha a kasashen na Afirka sai dai duk sukan yi kukan fuskantar kalubalen rashin jari da kuma samun gwarin gwiwa.