Martani kan jawabin shugaban Najeriya
August 1, 2023'Yan Najeriya dai na fatan Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai aiwatar da abun da ya fada, kar ya zama ya koma zakin baki kamar yadda aka shaida a baya. Muhimman abubuwan da su ka fi jan hankali a jawabin na shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu dai sun hadar da matsayin gwamnatinsa kan cire tallafin man fetur, wanda ya ce bai yi nadamar matakin ba da kuma bayyana kokarin da ya ke yi na rage wahalhalun da jama'a ke sha sanadiyyar cire tallafin. Haka kuma ya shaidar da cewa gwamnatinsa ta tara makudan kudi daga lokacin da aka dakatar da bayar da tallafin, abin ya ja hankulan masana da masharhanta da su ke ganin ba karamin kudi ba ne da za a iya yin amfani da su wajen saukake al'amura a kasa. Shugaba Tinubu ya kuma ce gwamnatinsa za ta samar da motoci masu amafani da sinadarin iskar gas, wanda za a yi amfani da su wajen rage farashin sufuri.
Sai dai wasu talakawan Najeriya dai sun bayyana cewa jawabin shugaban bai dada su da kasa ba, saboda babu wani sabon abu a ciki. Yayin da wasunsu kuma ke fatan za a gaggauta aiwatar da matakan da shugaban kasar ya ce zai dauka, musamman ma dangane da batun raba tallafin kayan abinci. Su ma a nasu bangaren, mamona sun yi marhabin da matakin shugaban kan batun samar da tallafin noma da raba abinci da aka ajiye domin sauke farashin abinci. Kungiyoyin kwadago a kasar kuma sun bayyana cewa, ba abun da su ka yi zato suka ji a wannan jawabin shugaban kasar ba. Game da batun karin albashin ma'aikata kuwa, Dakta Lawal Jafar Tahir da ke zaman malami a jami'ar jihar Yobe na ganin jawaban da shugaban ya yi na nuna kamar shugabannin Najeriya ba su san ma halin da al'umma ke ciki ba. Dangane da kokarin karfafa masana'antu da samar basussuka ba tare da kudin ruwa mai yawa ba kuwa, wani da kuma masanin tattalin arzikin kasa daga jami'ar Umaru Musa 'Yar Adua da ke Katsina, Dakta Murtla Abdullahi Kwara na da ra'ayin cewa kwata-kwata matakan da aka dauka ba za su yi wani tasiri kan halin da ake ciki ba.