Najeriya: Mahara sun sace mata 17 a Jihar Katsina
February 19, 2021Talla
Akasarin matan wadanda ke kan hanyar zuwa gidan biki na goye da kananan yara lokacin da lamarin ya faru. Al'ummar yankin dai na cigaba da kokawa kan dawowar hare-haren yan bindiga.
Har kawo yanzu 'yan bindigar basu ce uffan ba balle a san bukatunsu. Al'ummar na yankin fasakari na kokawa kan yadda suka ce duk da dumbin jami'an tsaron da aka jigbe a yankin bai dakatar da maharan cigaba da gudanar da sace mutane ba.
Jama'ar kananan hukumomin sabuwa da Dandume da Faskari sun ce babu ranar da za ta wuce ba tare da an kai wa daya daga cikin al'ummar yankunan hari ba.