Gwamnatin bayan fage a Najeriya
December 8, 2021Gamaiyyar 'yan boko ne dai tare da wasu 'yan siyasa suka ja gaba, wajen kadammar da gwamnatin ta bayan fage da suka bayyana cewa lokaci ya yi da ba za su ci gaba da yin shiru a kan yadda abubuwa suke tafiya a Najeriya ba. A cewarsu, dole ne su ceto kasar daga kalubalen da take fuskanta kama daga na rashin tsaro da koma bayan tattalin aziki da sauran dimbin matsaloli da ke kalubalantar al'umma.
Karin Bayani: Jega na son a yi watsi da jam'iyyun Najeriya
Farfesa Pay Utomi na cikin 'yan majalisar ministocin gwamnatin 'yan adawar ta bayan fage da aka kadammar a Abuja: "Najeriya tana cikin mumunan hali, dole mu fadawa kanmu gaskiya domin babu cikakken kamanta gaskiya da adalci daga bangaren gwamnati. Wannan iyakar gaskiya kenan, don haka dole ne mu dakatar da wannan matsalar. Mutane na shiga takara su samu mukami domin kawi su azurta kansu, kuma wannan na faruwa saboda ba wanda ke sa ido a kan abin da gwamnati ke yi."
Daya bayan daya ne dai suka bayyana sunayen mutanen da suka nada ministoci a majalisar zartaswar da suka kafa, wacce suka ce ba a karkashin wata jam'iyyar siyasa suka yi ta ba sai dai domin manufofinsu ya zo daya ne na batun samar da sauyi a kasar. A baya dai an ga bullar irin wadanan kungiyoyi na 'yan boko da wasu 'yan siyasa, kamar Save Nigeria Group da suka kalubalancin gwamnatin wancan lokaci.
Karin Bayani: Sabuwar jam'iyyar siyasa a Najeriya
Kafa gwamnatin jeka na yika ko kuwa ta bayan fage ta 'yan adawa a Tarayyar ta Najeriyar dai sabon al'amari ne a kasar, domin tun shekarar 1999 da kasar ta koma kan turbar dimukuradiyya ba a taba yin wannan ba. Abin jira a gani dai shi ne, ko shirye-shirye suke na rikida zuwa jam'iyyar siyasa ko kuwa adawa ce da za ta share hanyar shiga daya daga cikin jam'iyyun Najeriyar.