1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ikrarin nasara a yaki da ta'addanci

September 29, 2023

Rundunar tsaron Najeriya ta ce ta kusa kawo karshen rashin tsaro da ake fama da ita a wasu jihohi sai dai kuma wasu 'yan kasar na cewa har yanzu da sauran aiki.

https://p.dw.com/p/4Wz73
Sojan Najeriya a fagen fama
Sojan Najeriya a fagen famaHoto: STEFAN HEUNIS/AFP/Getty Images

'Yan ta'adda 200 ne dai rundunar tsaron tarrayar Najeriyar ta ce ta hallaka, ko bayan wasu 180 da doriya da ta ce na hannu, duk a cikin tsawon mako guda. A wani abun da sojan suke fadin na nuna alamun cin nasara a matsalar rashin tsaron da kasar ke fama da ita a halin yanzu.

Sojojin dai na takama da sabbin makamai na zamani da ke da damar kai hari daga nesa, wajen sauya akalar rikicin da a cewar sojan ke shirin zama tarihi cikin lokaci kankane.

Sojin Najeriya wagen yaki da Boko Haram
Sojin Najeriya wagen yaki da Boko HaramHoto: Lekan Oyekanmi/AP Photo/picture alliance

Air Commodore Edward Gebkwat dai na zaman kakakin rundunar sojan ta sama, rundunar da ke jagorantar sabuwar dabarar yakin. Koma ya zuwa ina sojan yake shirin zuwa cikin neman hada kan da kila kare rikici dai, sojojin sun share shekara da shekaru suna ta maharbi amma kuma wankin hula yana shirin kaisu dare a yaki da ta'addanci.

Karin Bayani: 'Yan Najeriya sun ce ba a murkushe ta'addanci ba

Dubban miliyoyin daloli ne dai tarrayar Najeriyar ta kai ga batarwa a kokarin samar da tsaron da ke zaman a kan gaba ga cigaban tattalin arziki da makomar kasar.

Jiragen yaki na sojin Najeriya
Jiragen yaki na sojin NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Tuni dai sabbabin yan mulkin Najeriyar suka fara nuna alamun gaza hakuri tare da yin gaban kai. Dikko Umar Radda dai na zaman gwamnan Katsina da ya ce jihar za ta kaddamar da sabuwar rundunar sa kai da nufin tunkarar rashin tsaron da ke addabar jihar.

Tun kafin Katsinan dai, an dauki lokaci ana karanta gazawa cikin rawar sojojin a yankuna daban daban cikin kasar can baya. Ana ma kallon ko in kular sojojin da ruwa dama tsaki da sace 'yan matan jami'ar tarraya ta Gusau.

Sabon matakin Katsinan dai a cewar Yahuza Getso da ke sharhi kan tsaron na iya kaiwa ga sauya da dama cikin batun rashin tsaro a jihar a nan gaba.