Najeriya: Farfado da shirin afuwa a Niger Delta
May 29, 2016Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da shirin sake farfado da matakin yin afuwa ga tsagerun Niger Delta a wani mataki na neman kawo karshen hare-haren da suke kaiwa kan cibiyoyin man fetur na kasar, da kuma ke haifar da koma baya ga aikin hakar man.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a cikin wani jawabi da ya gabatar a wannan Lahadi albarkacin zagayowar ranar cikon shekara daya da hawansa mulki.
A baya dai Shugaba Buhari ya sanar da takaice shirin yin afuwar dama dakatar da shi a karshen shekara ta 2018 kafin a halin yanzu ya sanar da sake farfado da shi a bisa a cewarsa dalillai na neman samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin mai arzikin man fetur.
Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa hare-haren baya-bayan nan da tsagerun suka kaddamar kan cibiyoyin aikin man, ba za su hana masu ba neman yin sulhu. Shirin yin afuwa da Najeriyar ta soma a shekara ta 2009 ya tanadi biyan albashi ga tsaffin mayakan yankin dubu 30 da kuma samar masu da aikin yi.