Najeriya ta sabunta alaka da Indiya
November 17, 2024Firaministan Indiya Narendra Modi da shugaba Bola Tinubu na Najeriya sun gana a wannan Lahadi a Abuja babban birnin Tarayya don sabunta abin da suka kira babban kawance tsakanin manyan kasashen Asiya da Afirka da ake wa kallon giwaye.
Karin Baynai: Najeriya ta nuna bukatar shiga kungiyar BRICS
A lokacin ganawar shugabannin, Narendra Modi ya ce hadin gwiwa tsakanin Indiya da Najeriya na da karfi sosai, kuma akwai sabbin damarmaki da za a kara karfafa dangantaka a fannoni da dama na ci gaba da suka hadar da kasuwanci da kuma tsaro.
Daga nasa bangare Shugaba Tinubu ya bai wa Modi lambar karramawa, sannan kuma ya yaba masa kan ingancin dimokuradiyyar kasar ndiya tare da yin alkawarin aiki tare bisa manufa daya da kuma mutumta juna.
Ziyarar ta da ke zama ta farko ta firamintan Indiya ke yi a Najeriya na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen biyu ke neman kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.
A daren Asabar ne dai Narendra Modi ya isa Abuja babban birnin Tarayya biya gayyatar Shugaba Tinubu, kuma hotunan da ya wallafa a shafinsa na X sun nuna yadda ya samu tarba mai kyau daga muhukunta da kuma 'yan asalin Indiya da ke zaune Najeriya wadanda yawansu ya kai mutum 60,000.