Matsaya tsakanin Najeriya da Ghana kan gas
October 20, 2015Kamfanin da ke lura da harkokin albarkatun mai a Najeriya ya bayyana cewa sun cimma daidaito da mahukuntankasar Ghana bayan da a baya kasar ta Najeriya ta yi barazanar cewa za ta tsaida albarkatun iskar gas da take ba wa Ghana wanda ke zama wani bangare na abin da take amfani da shi wajen bada wutar lantarki a kasar.
Kamfanin mai na NNPC a Najeriya ya ce sun cimma matsaya da Volta River Authority kan batun bashi sama da Naira miliyan miliyan dubu talatin da uku. Ohi Alegbe jami'i da ke magana da yawun kamfanin na NNPC a Najeriya ya ce baki dayan bashin da suka biyo mahukuntan na Ghana karkashin yarjejeniyar da suka cimma za a kammala biyan kudin zuwa watan Fabrairu na shekarar 2016.
Wannan yarjejeniya dai an kai ga cimmata ne bayan wani zama da aka yi tsakanin shugaban kamfanin na NNPC Ibe Kachikwu da shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama da ministan makamashin Ghana Kwabena Donkor.