1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNajeriya

Najeriya: CBN ya fara sa ido kan masu sana'ar POS

September 13, 2024

A ci-gaba da kokarin fuskantar ta’addanci, babban bankin Najeriya ya fara bin diddigin masu sana’ar POS, saboda hada-hadar takardar kudi na karkata musu maimakon bankuna, ciki har da kudin fansa bayan garkuwa da mutane.

https://p.dw.com/p/4kbZ3
Babban bankin Najeriya na daukan matakan tattalin arziki don yakar ta'addanci
Babban bankin Najeriya na daukan matakan tattalin arziki don yakar ta'addanciHoto: public domain

Sannu a hankali, hada-hadar takardar kudi a Najeriya na karkata daga bankuna zuwa masu sana'ar POS. Sai dai, ana dada kallon karuwar karbar kudaden fansa sakamakon ayyukan ta'addanci da ke ta'azzara a halin yanzu. Abin da ya kai kasar ga fara mai da hankali zuwa kafar POS, tare da Babban Bankin Najeriyar da fitar da wata  sabuwar sanarwar bin diddigin aiyyukan POS a kasar.

Karin bayani: Najeriya: CBN ya bada umarnin karbe kudaden ajiya na asusun da aka dade ba a amfani da su

CBN ya umarci manyan kamfanonin da ke harkokin POS da su rika bai wa babban bankin bayanai a duk wata na daukacin hada-hadar kowane POS da ke kasar a halin yanzu. Abuja na fatan bin diddigin kudaden fansa sakamakon ayyukan barayin daji da na birni da ke karuwa a cikin kafar POS. Sai dai da kamar wuya kwalliyar babban bankin ta kai ga biyan kudin sabulu, a tunanin Dr Surajo Yakubu dake zaman kwarrare  a laifukan kudi.

Karin bayani: Soke izinin canji: neman gyara ko kassara sana'a?

Kudi na taka muhimmiyar rawa wajen yaduwar ayyukan ta'addanci a Najeriya
Kudi na taka muhimmiyar rawa wajen yaduwar ayyukan ta'addanci a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Sama da POS miliyan biyu ne ke hada-hadar kudi a tudu da lungunan tarayyar Najeriyar. A bara kadai, kasar ta yi hada-hadar da ta kai ta sama da Tiriliyan 10 a cikin kafar POS, wannan na zama adadi mafi yawa kuma alamu na karuwar farin jinin kafar tsakanin al'umma.

Ana kallon POS a matsayin damar aiki da dubban daruruwa na 'yan Najeriya da ke kare karatu ba tare da damar ayyuka a kasar ba, kamar  matashi Nurrudeen Abubakar da ke sana‘ar POS bayan kare makaranta. A bara kadai, wata kididdigar da ba ta da tabbas ta ce an biya kudaden fansa da suka kai kusan Naira miliyan dubu 60 a jihar Sokoto ta POS, a  daya daga cikin tunga ta ayyuka na barayin dajin. Sai dai a tunanin Kyaftain Abdullahi Bakoji da ke sharhi kan batun tsaron, an bar jaki ana dukan taiki.

Karin bayani: Babban bankin Najeriya ya dauki mataki kan bankuna

Kungiyoyin ta'addanci na kai hare-hare da sace mutane don samun kudin fansa
Kungiyoyin ta'addanci na kai hare-hare da sace mutane don samun kudin fansaHoto: AFP/A. Marte

Najeriya na a tsakanin habaka hanyar aikin miliyoyin matasan da ke zaman kashe wando, da kuma tinkarar rashin tsaron da ke da ruwa da tsaki da kudade na haramun.