Najeriya: Bikin Easter cikin tsauraran matakan tsaro
March 30, 2018Dubun-dubatar mabiya addinin kirista a jihohin arewa maso gabashin Najeriya sun yi fitar dango zuwa majami'u cikin ko dai sabbin kaya ko kuma wankakku domin yin addu'o' da wakokin yabo a wani bangare na bukukuwan Easter na bana. Ga misali a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno an samu fitar jama'a zuwa majami'u domin wannan bikin na Easter sabanin shekarun baya da mutane suka noke a gidajen su saboda fargabar hare-hare da ake alakantawa da Boko Haram ya haifar a shiyar.
Sauran yankuna da ake da zaman lafiya ma kamar kudancin Borno mabiya addinin kirista sun a gudanar bukukuwan cikin kwanciyar hankali ba kamar shekarun baya ba. A ziyara da wakilin DW ya kai daya daga cikin majami'u da ke Maiduguri ya tarar da mabiya addinin kirista suna addu'o'i da wakoki na yabo.Haka labarin yake a sauran jhohin Adamawa da Bauchi da Gombe da Taraba da Yobe inda nan ma ake bukukuwan cikin kwanciyar hankali.
Sai dai ana bukukuwan ne cikin tsauraran matakan tsaro inda jami'an tsaro na gwamnati da matasa da ke kula da tsaro a coci-coci da ke kafa shingen suna bincika duk mai shiga tare da amfani da na'urori don tabbatar da ba a shiga da wani abu da zai cutar da jama'a ba. Mabiya addinin kirista sun samu damar yin tafiye-tafiye zuwa garuruwa da kauyukan su na asali domin alamta wannan rana da kuma yin bukin cikin ‘yan uwa da abokan arziki don kara dankon zumunci.