1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an tsaron Najeriya ta ceto mutane daga Boko Haram

Ramatu Garba Baba
June 5, 2018

Rundunar tsaron Najeriya ta ce wasu mata kusan 60 na daga cikin mutanen da ta yi nasarar 'ceto su a hannun kungiyar Boko Haram kuma a ciki akwai wasu 'yan mata biyu da aka gano na dauke da juna biyu.

https://p.dw.com/p/2ywGd
Nigeria Boko Haram Anschlag in Maiduguri
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

A sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce matan sun kasance wadanda mayakan suka yi garkuwa da su tare da mayar da su bayi da kuma yin lalata da su. Akwai wasu yara kimanin 70 da maza 15 baya ga matan da aka ceto a wani samame da rundunar ta kaddamar kan mabuyar mayakan da ke a garin Modu Kinetic na Jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya a ranar Lahadin da ta gabata.

Rundunar ta ce mazan suma an yi ta bautar da su ganin yadda ake saka su yin aikin karfi a tsawon lokacin da suka yi a hannun kungiyar. Tuni aka kai mutanen sansanin 'yan gudun hijira inda aka tsugunar da wadanda rikicin na Boko Haram ya galabaita.