1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Amurka da Faransa a Najeriya

May 6, 2024

A wani abu da ke zaman kokarin aiken sako, 'yan boko da jam'iyyun adawa sun ce a kai kasuwa kan batun mayar da sansanonin sojan Amurka da Faransa zuwa Najeriya.

https://p.dw.com/p/4fYLg
Nijar | Agadez | Sojoji | Amurka | Faransa
A baya dai, sojojin Amurkan na da sansani ne a birnin Agadez na Jamhuriyar ta NijarHoto: Alex Fox Echols Iii/Planetpix/Planet Pix via ZUMA Wire/picture alliance

Can a takarda dai har ya zuwa yanzu masu mulkin Tarayyar Najeriya, ba su ayyana aniyarsu ta karbar sojojin Faransa da na  Amurka da gwamnatin juyin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar ta kora ba. To sai dai kuma kama daga 'yan boko ya zuwa jam'iyyun adawa, daukacin Najeriyar ta dauki dumi dangane da kafa sansanonin sojojin kasashen guda biyu a kasar.

Karin Bayani: Nijar: Ko alaka da Faransa ta zo karshe?

Juyin mulkin na Nijar da ma bakar siyasar yankin ce dai, ta kai ga rushe sansonin da ke da tasirin gaske cikin batun tsaro da ma siyasar yankin Sahel. To sai dai kuma daga dukkan alamu kokarin mayar da sojojin Amurkan da na Faransa zuwa makwabciyar kasa Tarayyar Najeriyar, ya haifar da muhawara mai zafi cikin kasar da ke fadin ba hali. Duk da burin inganta tsaro cikin yankin Sahel din dai, kwararru cikin kasar da daman gaske na kallon sansanonin sun saba ka'ida ta siyasa da ma batun tsaron al'ummarta.

Nijar | Yamai | Sojoji | Kora | Faransa
Sojojin Faransa ne dai gwamnatin juyin mulkin sojan ta Nijar ta fara fatattakaHoto: Sam Mednick/AP Photo/picture alliance

Farfesa Kamilu Sani Fagge dai na zaman kwarrare ga batun siyasa ta kasar da kuma ya ce, irin alakar da ake shirin da a kulla ba ta taimaki kasashen da suka kulla ta a baya ba. A baya  dai Najeriyar ta yi nasarar kulla kawancen tsaro da Ingila a kan batun  tsaron a shekaru 1960, adawa da muradin gwajin jiragen na Ingila a kasar ya tilasawa gwamnatin Tafawa Balewa soke yarjejeniyar mai tasiri. Kokari na sake kulla sabuwar yarjejeniyar tsaron da Amurka a gwamnatin Olusegun Obasanjo ta kare ba nasara, sakamakon adawar manyan hafsoshin tsaron Najeriyar.

Karin Bayani: Masu adawa da kawance kasashen Sahel

Shi ma dai Umar 'Yar Adua ya sa kafa ya yi fatali da kokarin Amurkawan, na kafa shalkwatar rundunarsu da ke kula da kasashen Afirka. Kabiru Adamu dai masani ne kan harkokin tsaro kana kuma shugaban kamfanin Beacon Consult da ke taka rawa cikin batun tsaro a yankin Sahel, kuma ya ce muradun na kasashen biyu na iya sabawa da tunanin da ke akwai na samar da tsaron. A cikin watan Disambar bara ne kasar Faransa ta kulle sansanin sojojinta da ke Nijar din, bayan kwashe dakarunta 1,500. A yayin kuma da Amurka ke shirin kwashe nata  sojojn 1,000, bayan share shekaru 11 a Jamhuriyar ta Nijar.