1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar wani ɗan jarida a Maiduguri

October 24, 2011

'Yan sari ka noƙe sun hallaka Zakariya Isa wani ɗan jarida mai aiki a gidan talbajan mallakar gwamnatin Tarayyar Najeriya

https://p.dw.com/p/12xo6
Hoto: AP

Wasu mahara sun hallaka wani dan Jarida mai suna Zakariya Isa a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno mai fama da rikici bayan sun buɗe masa wuta da muggan bindigogi yayin da yake shiga gidansa ranar Asabar da dare.

Wannan ɗan Jaridar Zakariya Isa dake aiki a gidan Talabijin mallakar gwamnatin tarayyar ƙasar ya gamu da ajalinsa bayan buɗe masa wuta da muggan bindigogi da wasu da ba'a tantance ko su waye ba suka yi.

Wanda ke Maƙobtaka da shi a unguwar Bulunkutu a garin na Maiduguri kamar Malam Mai Dala'ilu, sun bayyana cewar mamacin ya fito masallaci ne bayan sallar Isha'I inda yayiwa mutane bankwana da nufin shiga gida kafin gamuwa da ajalin sa.

Malam Sakariya Isa wanda sannane ne saboda aikin fassara da karanta Labarai a hukumar gidan Talabijin ta tarayya dake Maiduguri shine ɗan Jarida na farko da aka hallaka tun lokacin da aka fara rigingimu da tashe-tashen hankula a Maiduguri.

Wannan kisan gilla da aka yi masa ya tada hankalin sauran ‘yan Jarida ganin irin wannan kisa na sari-ka-noke ya fara iso su kamar Malam Ibrahim Pantami ma'aikaci a kafar yaɗa labarai mallakar jihar Gombe ya shaida.

Su ma ƙungiyoyin kare haƙƙin bani Adama sun bayyana takaicinsu dangane da wannan kisar wanda suka ce mai tsananin tada hankali ce.

Alhaji Abba Muhammad Gwani, shine shugaban ƙungiyar kare haƙƙin bani Adama da CLO a Gombe.

Kimanin mutane 15 aka yi kiyasin an hallaka a cikin mako guda kacal, a irin wannan hare-hare na sari ka noƙe a wani sabon salon rigima da al'ummar Maiduguri su ka tsinci kan su a ciki.

Za ku iya sauraran rahotani biyu daya daga wakilinmu na Gombe Al-amin Suleiman game da kisan sai kuma na biyu wanda martanin jama´a ne daga Babangida Jibril

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Halima Balaraba Abbas