Mutun daya ya mutu a harin teku a Gabon
December 22, 2019Talla
Rahotanni daga kasar Gabon sun ce wasu maharan teku a birnin Libreville sun kaddamar da wani hari kan wasu jiragen ruwa hudu tare da kashe wani babban Kwamandan sojan ruwa dan kasar Gabon, sannan suka yi garkuwa da wasu ma'aikatan jiragen 'yan kasar Chaina hudu.
Tuni kakakin gwamnatin kasar ta Gabon Edgard Anicet Mboumbou Miyakou ya tabbatar da aukuwar lamarin a yayin wani jawabinsa a faifan bidiyon da aka wallafa, yana mai cewa harin ya auku ne a daren Asabar zuwa yau Lahadi, tare da bayyana jumamin mutuwar dan kasar ta Gabon guda.