Mutane sun mutu a hare-haren Maiduguri
November 16, 2017Talla
Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu jerin hare-haren da 'yan kunar bakin wake hudu suka kaddamar a birnin Maiduguri, sun halaka mutane akalla 18 yayin da wasu 29 suka jikata. Shaidu sun ce harin na yammacin ranar Laraba, ya kasance cikin mafiya muni da aka gani a birnin a bana.
Kakakin rundunar kakakin jami'an 'yan sanda a Borno, Victor Isukwu, ya ce maharan maza biyu mata biyu, sun afka wa wani waje ne mai yawan masu hada-hada a 'Muna Garage'. Harin na farko a cewar 'yan sandan an kaddamar da shi a wani wajen da mutane ke Salla, kuma maharan hudu sun mutu.
Hare-haren dai na zuwa ne yayin da rahotanni daga yankin Madagali dake arewacin jihar Adamawa ma ke tabbatar da wani harin na Boko Haram a yankin da yammacin na Laraba.