Mutane shida suka mutu a tekun Libiya
April 16, 2022Talla
Hukumar kula da kauran jama'a ta duniya ta gano gawawakin wasu mutane 6 bayan da wani kwale-kwalen katako dauke da bakin haure kimanin 35 ya kife a gabar ruwan Libiya. Kawo yanzu dai ana ci gaba da neman wasu mutane 29 da suka yi batan dabo.
Ko a makon da ya gabata ma kimanin bakin haure 53 aka bayar da rahoton sun mutu a gabar ruwan Libiyan a cewar hukumar. Kasar Libiya da ta kwashe gomman shekaru ta na fama da rikici na zama matattara ta 'yan Afrika da nahiyar Asiya da ke son tsallakawa zuwa Turai ba bisa ka'ida ba.
Alkalumman Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewa kimanin bakin haure fiye da dubu 1 ne suka nutse a tekun Bahar rum a shekarar bara.