1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun rasu a wani wurin ibada a Indiya

Salissou BoukariAugust 10, 2015

Mutane fiye da 10 sun rasu a kasar Indiya, sakamakon cinkoson da ya haddasa ture-ture a wurin ibada na 'yan Hindu, inda suka saba kai ziyara.

https://p.dw.com/p/1GCVv
Hoto: Getty Images/AFP/Str

Akalla mutane dubu 150 ne da suka ja layi, suka nemi shiga wurin ibadar da gudu lokacin da aka buda kofofinsa, abun da ya haddasa ture-ture, tare da tattake mutane da dama a cewar wata majiya ta 'yan sandar kasar Indiya. Majiyar ta kara da cewa, daga cikin mutane 10 da suka rasu akwai mace daya, sannan wasu mutane akalla 20 sun samu raunuka. A watan Yuli ma dai da ya gabata akalla mutane 27 ne suka rasu yayin wani ture-ture da ya wakana bakin wani tabki na Godavari da ke tsakiyar kasar ta Indiya inda dubunnan mutane ke zuwa yin wanka na al'ada.