1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun mutu a Somaliya

October 30, 2022

Hukumomi a Somaliya, sun ce gomman rayuka ne suka salwanta a alkaluman da ake samu daga tarwatsewar da wasu nakiyoyi suka yi a ranar Asabar.

https://p.dw.com/p/4IqMV
Hoto: Farah Abdi Warsameh/AP/picture alliance

Shugaba Hassan Sheikh Mohamud na kasar Somaliya, ya ce kawo i yanzu alkaluman wadanda suka salwanta a hare-haren boma-bomai da aka kaddamar a kasar ya kai mutum 100.

Da ranar jiya Asabar ne dai wasu motoci biyu shake da nakiyoyi suka tarwatse a kusa da ma'aikatar ilimi da ke a Mogadishu babban birnin Somaliyar.

Bayanai daga cibiyoyin kula da lafiya na cewa wadanda suka jikkata a lamarin sun zarta mutum 300.

'Yan sanda sun ce wasu mutane hudu ne suka kaddamar da harin cikin motocin biyu, kuma fararen hula ne abin ya fi rutsawa da su.

Boma-boman sun kuma tashi ne a daidai lokacin da gwamnatin Somaliya ke shirye-shiryen fara tattaunawa kan sabon salo na yaki da ta'addanci.

Kungiyar mayakan tarzoma ta al-Shabab mai alaka da al-Qaida, na rike da yankuna da dama na tsakiya da ma kudancin kasashen yankin kusurwar Afirka, kuma ta ce ta kai harin ne saboda ma'aikatar ilimin kasar na karbar tallafi daga kasashen da ba na Musulmi ba.