1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 23 sun mutu a hadarin jirgi a Indiya

Ramatu Garba Baba ATB
August 19, 2017

A kasar Indiya akalla mutane 23 yanzu aka tabbatar da mutuwarsu a wani hadarin jirgin kasa na fasinjoji da ya auku a yankin Uttar Pradesh da ke arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/2iVut
Indien Zugentgleisung in Muzaffarnagar
Hoto: picture alliance/ZUMAPRESS.com

A kasar Indiya akalla mutane 23 ne yanzu haka aka tabbatar da mutuwarsu a wani hadarin jirgin kasa na fasinjoji da ya auku a yankin Uttar Pradesh da ke arewacin kasar. Mai magana da yawun ma'aikatar sufurin yankin Neeraj Sharma ya ce taragwon jirgin shida ne suka kauce daga hanya, lamarin da ya janyo asarar rayukan mutane  fiye da ashirin tare da raunata wasu tamanin da daya.

Ana ci gaba da aikin ceto mutanen daga cikin tarkacen jirgin a hadarin da ya auku a wannan Asabar. A bara ma dai fiye da mutane 100 ne suka mutu a jihar ta Uttar Pradesh sakamakon hadarin jirgin kasa. Hadarin jirgin kasa a Indiya ya zama jiki ganin rashin ingancin layukan dogon da ake anfani da su da aka ce duk sun riga sun tsufa.