Mutane 22 sun mutu a turmutsitsi a Indiya
September 29, 2017Talla
An dai samu turmutsitsin ne a lokacin da wani tarin jama'a suke kokarin sauka daga wata matattatakala da ke zuwa tashar jiragen kasa ta Elphinstone. Babban daraktan asibintin KEM inda aka kai mutanen da suka jikkata Avinash Supe, ya ce sun kidaya gawarwaki 22. Mai magana da yawun tashoshin jiragen kasa na kasar ta Indiya ya ce mutanen da ke nemen shiga jirgin, sun bi wannan hanya ce gabaki dayansu a kokarinsu na gujewa ruwan sama kamar da bakin kwarya da ke sauka a daidai lokacin. Cikin wani sako da ya aike ta shafinsa na Tweetter Firaministan kasar ta Indiya Narendra Modi ya nuna alhininsa tare da isar da ta'azziya ga iyalan marigayan.