1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 18 sun mutu wajen jana'aiza a indiya

January 18, 2014

Kimanin mutane 18 sun mutu a sakamakon wani turmutsutsu da aka samu yayin jana'izar da aka yi wa wani malamin addinin Islama a birnin Mumbai na kasar Indiya.

https://p.dw.com/p/1At6h
Taron mutane lokacin jana'izar Muhammad Burhanuddin
Hoto: Reuters

Kamfanin dillancin labarai na Press Trust na kasar ta Indiya, ya ce baya ga wanda suka rasu, hukumomi sun tabbatar da jikkatar mutane 40 a wajen jana'izar ta Muhammad Burhanuddin, wanda ya rasu a jiya Juma'a ya na da shekaru 102.

Wannan asarar rayuka da ma jikkata da aka samu a kasar ta Indya dai, na zuwa ne watanni kalilan bayan da wasu mutane 115 suka kwanta dama, sakamakon turereniya da aka yi a wani waje na bauta na mabiya addinin Hindu. Kana wasu daruruwa da suka rasu tsakanin shekarar ta 2008 zuwa 2011, batun da ya sanya mahukuntan kasar ke ci-gaba da nuna damuwarsu, dangane da wannan lamarin da ke faruwa daga lokaci zuwa lokaci a kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman