Jirgin saman Indiya ya yi hadari a Kerala
August 7, 2020Talla
Masu aiko da rahotanni sun ce jirgin ya fito ne daga Dubai dauke da passinjoji 185 kafin daga bisani wata matsalar ta tilasta masa yin saukar gagawa a filin jiragen sama na jihar Kerala.
Tuni dai kafafen yada labarun Indiya suka ruwaito cewa gwamman mutane na can kwance a asibiti sakamakon hadarin.