1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmi sun yi hawan Arfat na Hajjin bana

Gazali Abdou tasawaSeptember 23, 2015

Tun da sanhi safiyar wannan Laraba miliyoyin alhazzai ke ta tururuwa zuwa hawan dutsen na Arfat mai tsawon mita 70 da kuma ya ke a matsayin kololiwar aikin ibada daga cikin jerin ayyukan ibadar aikin Hajji .

https://p.dw.com/p/1GbnD
Muslime beten am Berg Arafat 03.10.2014
Hoto: AFP/Getty Images/M. Al-Shaikh

Yau take ranar Arfat a kasar Saudiyya inda tun da sanhi safiya miliyoyin alhazzai suka yi ta tururuwa zuwa hawan dutsen na Arfat mai tsawon mita 70 da kuma ya ke a matsayin kololuwar aikin ibada daga cikin jerin ayyukan ibadar aikin Hajji wanda ya ke daga cikin manyan shika-shikan muslunci guda biyar.

Alhazzan dai wadanda ke a cikin farfarun tufafin harami za su share tsawon yinin wannan rana ta Arfat suna gudanar a cikin kaskantar da kai da fana'i addu'o'i da nafilfili a saman dutsen mai albarka wanda a samansa ne, karni 14 da suka gabata Annabi Muhammadu ya gabatar da hudubarsa ta ban kwana.

Alhazzai sama da miliyon biyu ne dai daga kasashe daban daban na duniyar Musulmi suka halarcin aikin Hajjin na shekarar bana a kasa mai tsarki. Aikin Hajjin na bana na gudana ne a cikin wani yanayi na tsanananin zafin rana. Sai dai rahotanni daga kasar ta Saudiyya na cewa kawo yanzu aikin Hajjin na gudana ba tare da wata matsala ba.