Musulmi na gudanar da babbar Sallah ta 2024
June 16, 2024Al'umma Musulmi a fadin duniya na gudanar da babbar Sallah ko kuma Sallar Layya a wannan Lahadi a daidai lokacin da mahajjata kusan miliyan biyu ke karkare ibadar aikin Hajji na bana a birnin Mina na Saudiyya tare da 'Jifan shedan' wannan ke zama ranar farko ta 'Eid al-Adha'.
A daidai wannan lokaci ne Musulmi ke hawa idi a wannan safiya ta 10 ga watan Zulhijja domin yin raka'o'i biyu na nafila kafin daga bisani wadanda Allah ya horewa su yanka dabbobi su ci kuma su yi sadaka kamar yadda ibadar ta samo asali daga Annabi Ibrahim Alaihissalam ta tanadar.
Karin bayani: Muhimmancin layya a addinin musulunci
Nan gaba kadan ne a kasashe irinsu Najeriya da Nijar, da Ghana da Kamaru da dai sauransu za a yi hawan Idin Sallar wacce a bana ta riski al'umma da dama cikin yanayi na tsadar rayuwa da kuma tashe-tashen hankula.
Kamar a sauran kasashen duniya anan ma Jamus Musulmi na gudanar da babbar Sallar ta Musulunci kuma tuni aka kammala sallar idi a masallatai daban daban na kasar.
A yanki Gabas ta Tsakiya kuwa babbar Sallar ta bana ta zo ne a daidai lokacin da ake gwabza yaki a zirin Gaza na Falasdinu biyo bayan barkewar rikici da ya ki ya ki cinyewa tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas.