Murnar soke dokar hana luwadi a Indiya
September 6, 2018
Tarin 'yan madigo da 'yan luwadin sun yi ta rugumar juna da kururuwar murna lokacin da kotun ta sanar da hukuncin halarta wannan masha'a a kasar. Krishanu wani dalibi a jami'ar birnin New Dehli daya daga cikin 'yan luwadin ya bayyana farin cikinsa da matakin kotun yana mai cewa:
Ya ce "Na rasa yadda za ni bayyana farin cikina, ba ni da kalmar da zan fada da za ta iya fassara farin cikin da nake ji a zuciyata, lallai karamin mataki ne amma mai cike da tasiri"
A baya dai wata doka da kasar ta Indiya ta gado tun a lokacin mulkin mallaka ce ta haramta luwadi da madigo a kasar inda ake iya yanke wa mutuman da aka kama da aikata wannan laifi hukuncin daurin rai da rai. Sai dai ba safai alkalan kasar ke aiki da dokar ba inda a tsawon karni daya da rabi da dokar ke nan, mutanen da aka taba tuhuma ba su kai mutun 200 ba.
Akasarin 'yan kasar ta Indiya musamman mazauna yankunan karkara na kallon akidar luwadi da madigo a matsayin wani nau'i na tabin hankali. Kuma yanzu haka kasashe sama da 70 a duniya suka haramta wannan akida ta mu'amalar masu jinsi daya a cikinsu.