1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump bai ji dadin abin da ya faru ba

January 14, 2021

Sabanin ra'ayoyi tsakanin Amirkawa bayan da majalisar dokoki ta tsige Shugaba Donald Trump daga kan mulki, sati guda kafin cikar wa’adin mulkinsa, bayan da ta tuhume da shi laifin tunzura masu bore.

https://p.dw.com/p/3nuhD
USA Präsident Trump spricht vor Anhängern über die Berufung von Kavanaugh an den Obersten Gerichtshof
Hoto: Reuters/Y. Gripas

Kakakin majalisar dokokin Amirka Nancy Pelosi lokacin da take magana ta tabbatar da cewar, an zartar da kudirin da aka cimma a kan Trump, tana mai cewar, babu wanda ya fi karfin doka, ko da kuwa shugaban Amirka ne. Ko da yake kudirin ya samu karbuwa da goyon bayan dukkan ‘yan Demokrats, a wannan karon har da wasu wakilai 10 na jam’iyyar Trump ta Republican, amma a dunkule a muhawarar da aka tafka kafin kuri’ar, ‘yan Republican sun zargi Demokrats da yin gaugawa, da rashin adalci wa Trump da kuma munafucii, yayin da su kuma Demokrats suka dage kan cewa, Trump ya gaza, ya yi abin kunya kuma babban laifi ne, duba da irin barnar da aka tafka a farmakin da aka kai majalisar. A halin da ake ciki dai, kamfanoni da cibiyoyi dabam-dabam suna cigaba da soke kwantaragin kasuwanci na milyoyin daloli da suka kulla da kamfanonin Trump, a dai-dai wannan lokaci da ake cigaba da mayar da shi saniyar ware, lamarin da ake hasashen cewa, zai iya yin mummunar illa, ko ma ya zama dalinlin karayar arzikinsa.