1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MSF: Yunwa na barazanar halaka yara a Najeriya

March 12, 2024

Kungiyar Doctors Without Borders ta ce yunwa na neman haifar da mummunan yanayi a Najeriya, inda tuna cutar tamowa ta fara barkewa a jihohin da ke fama da 'yan bindiga.

https://p.dw.com/p/4dPcJ
Hoto: Ben Curtis/AP/picture alliance

Kungiyar likitoci ta kasa da kasa, "Na Gari na Kowa", ta Doctors Without Borders da ake wa lakabi da MSF ta yi gargadin samun mummunan yanayi da ci gaba da tabarbarewar ayyukan agaji a jihohin da ke arewa maso yammacin Najeriya. Kungiyar ta ce a jihohi biyar kadai na wannan yanki na Najeriya ta duba lafiyar kananan yara sama da 170,000 da ke cikin matsananciyar yunwa a shekarar da ta gabata, baya ga wasu yara 32,000 da ta kwantar asibitoci a sabili da yunwar da rikicin 'yan bindigaya haifar.

Hakan na zuwa ne a yayin da kungiyar Amnesty International ta ce a makon da ya gabata kadai an yi garkuwa da mutum kusan 700 a arewacin Najeriya, alkaluman da wasu masu sharhi ke cewa ba a taba samunsu ba a cikin 'yan shekarun nan.

Kawo yanzu hukumominm jihar Kaduna, inda aka sace dalibai a makarantun kauyen Kuriga da na jihar Borno, inda aka yi garkuwa da mata 'yan gudun hijira har ma da jihar Sokoto, inda aka shiga aka shiga wata makarantar Allo aka yi awon gaba da almajirai na cewa suna iyakar kokarinsu wajen dawo mutanen ba tare da wanilahani ba.