Mr Kurt Beck ya ci alwashin dawo da kimar SPD a Jamus
April 11, 2006Mai jiran gadon karbar shugabancin ragamar jam´iyyar SPD a nan Jamus, wato Kurt Beck yayi alkawarin ci gaba da kasancewar jamiyyar sa a cikin gwamnatin hadaka da jamiyyar CDU, da shugaba Angela Merkel ke shugabanta.
A cikin wata hira da yayi da yan jaridu, Mr Kurt Beck yaci alwashin ci gaba da daukar matakan dawo da darajar jamiyyar sa ta SPD, don samun karbuwa yadda yakamata a tsakanin Jamusawa.
Ya zuwa yanzu dai Mr Kurt Beck yaki ya tabbatar da ko zai kalubalanci, shugaba Angela Merkel ko kuma akasin haka a zaben gama gari da za a gudanar a shekara ta 2009.
Ana dai sa ran tabbatar da Mr Kurt Beck , a wannan mukami ne na shugabancin jamiyyar ta SPD a ranar 14 ga watan mayu na wannan shekara da muke ciki.
Rahotanni dai sun nunar da cewa, kasancewar Mr Kurt Beck a matsayin shugaba mai jiran gado, ya biyo bayan murabus din shugaban jamiyyar ne na SPD, wato Matthias Platzeck ne daga mukamin , bisa dalilai na rashin koshasshiyar lafiya.