1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Motsa jiki tsakanin Matasan Dosso

Ramatou Issa OuankeMay 18, 2016

A jihar Dosso na Janhuriyar Nijar, wata matashiya ta bude gidan motsa jiki wanda kuma ya samu karbuwa musamman tsakanin matasa da mata.

https://p.dw.com/p/1IphB
Videostill AOM Africa on the Move Tansania Gemeinde Hilfe für Kinder mit Behinderung
Hoto: DW

Mai shekaru 35 ita Haoua Sani Ibrahime wadda aka ma lakabi da sunan Santia ta kasance mace ta farko da ta yi nasarar bude gidan horas da Tayekondo a Jihar Dosso, kuma ta bayyana dalilan da suka kaita da daukan wannan matakin ma'ana bude Klub

To sai dai a cewar Haoua kasancewar ta matar aure kuma a kasar da addinin musulunci ke da karfi, wasu suna wa wannan aikin nata wani kallo na daban.To amma duk da wannan matsalolin da Santia take fuskanta daga wasu mutane wannan bai hana ta samun ci gaba a cikin wannan aiki nata ba.

Kusan dai matasa maza da mata 51 ne ke samun horo a Klub din. Su dai wadannan matasan sun bayyana dalilan da ya sa su shiga wannan Klub kin don samun horo.

Ita dai Haoua ta bayyana cewar tana samun goyan baya sosei daga hukumomin jihar ta Dosso kuma yanzu haka tana shirin bube gidan motsa jiki na matan aure.