1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen taron muhalli na Paris

Lateefa Mustapha Ja'afarDecember 7, 2015

Ministocin muhalli na kasashen da ke halartar taro kan batun sauyi ko kuma dumamar yanayi a birnin Paris na kasar Faransa sun karbi ragamar aiwatar da yarjejeniyar shawo kan matsalolin da ke tattare da batun.

https://p.dw.com/p/1HIuX
Taron sauyi ko kuma dumamar yanyi na Paris
Taron sauyi ko kuma dumamar yanyi na ParisHoto: M. Ralston/AFP/Getty Images

Ko da yake sun rage burunkan da suke da shi a kan batun sai dai kafin a kai ga aiwatar da burukan da aka mayar da hankali a kansu a yanzu akwai sauran tafiya. Tashin farko dai za a iya cewa akwai alamun samun nasara a taron na birnin Paris ganin cewa daga cikin matsaloli sama da 2500 da aka gaza warware wa a baya 567 ne kacal suka rage yanzu, ko da yake su ne manyan matsalolin da suka zamo wajibi a shawo kan su. Wadannan matsaloli kuwa za a iya magance su ne kawai a siyasance. Al'ummomin kasa da kasa dai sun damu gaya kan batun sauyi ko kuma dumamar yanayin, koda a karshen mako sai da shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis ya yi addu'ar fatan cimma nasara a wannan taro na birnin Paris. A cewar wakilin kungiyar kare muhalli ta "Green Peace" Martin Kaiser a yanzu ne za a shiga muhawara mai zafi. Ita kuwa wata kwararriya a kan muhalli kuma shugabar sashen kula da muhalli ta asusun kare haluttu reshen Jamus Regine Günther cewa ta yi ko dai tattaunawar ta yanzu ta fitar da sakamako mai kyau ko kuma ta zamo tamkar abin dariya. Ta kara da cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba:

Zanga-zanga a farfajiyar taron dumamar yanayi na Paris
Zanga-zanga a farfajiyar taron dumamar yanayi na ParisHoto: Reuters/E. Gaillard

Ta ce:"Kasashen da suka fi fuskantar barazanar sauyin yanayi sun daga muryoyinsu a nan, sun nunar da cewa me zai sa su cimma yarjejeniyar da za ta sanya su cikin matsala? Har yanzu ba a tattauna wannan matsala ba kuma a tunanina yana da kyau yin hakan."

Rarrabuwar kawuna a zauren taro

Akwai dai rarrabuwar kawuna tsakanin kasashe masu tasowa wadanda suke fama da talauci kana matsalar dumama ko kuma sauyin yanyin tafi shafa da kuma masu karfin tattalin arzikin masana'antu da ke fitar da gurbatacciyar iska wadda aka hakikance ita ce ke haddasa dumamar yanayi a duniya. Har yanzu akwai sauran rina a kaba kan batun bada tallafin kudi ga kasashen da suka fi fuskantar barazanar sauyi ko dumamar yanayin. Kasashen da ke da karfin arzikin masana'antu dai sun sha alawashin biyan makudan kudade duk shekara abin da kuma kasashe masu tasowar ke tantama a kai. Ga dukkan alamu dai kasashe masu tasowa a shirye suke su rage yawan gurbatacciyar iskar da suke fitarwa misali kananan tsibirai biyar da suka fi fuskantar barazanar sauyin yanayin sun amince da rage zafin da ake samu a duniya zuwa digiri daya da rabi a ma'aunin celsius wanda tun da farko ba haka taron na birnin Paris ya tsara ba. Gabanin taron an tsara cewa za a amince ne da rage zafin zuwa digiri biyu a ma'aunin celsius kamar yadda taron share fage da aka gudanar a birnin Lima ya amince. A cewar sakataren ma'aikatar muhalli ta Jamus Jochen Flasbarth, wadannan tsibirai na fitar da wani babban sako ne ga duniya.

Ya ce: "Mun amince da rage zafin zuwa digiri biyu a ma'aunin celsius a Lima. Yanzu zamu iya fahimtar cewa ga kananan tsibiran na duniya digiri biyun ba zai magance musu barazanar da suke fuskanta daga dumamar yanayi ba. A nan in har za a maye gurbin batun digiri biyun da digiri daya da rabi dole sai an yi amfani da fasaha wanda shi ma tilas a samu matsala daga wasu bangarori misali, inda za a ringa tara hayakin mai guba wato "Carbon capture and storage" CCS."

Sakataren ma'aikatar muhalli ta Jamus Jochen Flasbarth
Sakataren ma'aikatar muhalli ta Jamus Jochen FlasbarthHoto: picture-alliance/dpa

Kalubale mai yawa ga Tsibirai

A cewar Firaministan Tsibirin Tuvalu Enele Sopoaga tuni al'ummar kasarsa ke fuskantar matsalar dumamar yanayi, inda ya ce:

"Tuni muka fara dandana azabar da dumamar yanyi ke haifarwa. Uku daga cikin tsibiranmu basu da abinci da tsabtataccen ruwan sha. Haka kuma duk kayan amfanin gonar da suka shuka sun lalace bayan afkuwar mahaukaciyar guguwar Pam. Ba ka tunanin wannan gargadi ne a garemu? Duk wani karin dumamar yanayi da za a samu babban bala'i ne."

A cewar Luz Gallagher mai magana da yawun kungiyar "The Climate Action Network" (CAN) da ke da kungiyoyi masu zaman kansu kimanin 900, nasarar da aka samu ta kokarin cimma matsaya wani abin farin ciki ne koda ya ke ta ce akwai artabu mai yawa a tattaunawar cikin wannan mako.