1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan harkokin wajen Gabon ya mutu

Ramatu Garba Baba
January 20, 2023

Fadar gwamnatin kasar Gabon ta sanar da mutuwar ministan harkokin wajen kasar Michael Moussa Adamo bayan da ya yanke jiki ya fadi a yayin wani taron 'yan majalisu.

https://p.dw.com/p/4MUpo
Michael Moussa Adamo
Michael Moussa Adamo Hoto: Dimitrios Karvountzis/Pacific Press/IMAGO

Fadar gwamnatin Gabon ta sanar da mutuwar ministan harkokin wajen kasar Michael Moussa Adamo, sanarwar gwamnatin ta ce, Moussa ya mutu ne a sakamakon ciwon bugun zuciya da ya riske shi a yayin da ake shirin zaman majalisa a wannan Jumma'ar.

 Ministan dan shekaru sittin da biyu da haihuwa, ya kasance makusancin shugaban kasar Ali Bongo Ondimba da ya kwashi shekara da shekaru yana mulkin kasar da ke tsakiyar Afirka. Shugaba Bongo ya baiyana shi a matsayin amininsa yana mai cewa, kasar ta yi rashin dan kasa mai kishin al'ummar. Kafin mutuwarsa dai, Moussa Adamo ya taba rike mukamin ministan tsaron kasar da kuma jakadan Gabon a kasar Amirka.