Zargin lalata ya sauke minista a Indiya
October 17, 2018Talla
Minista Mobashar Jawed Akbar ya yi murabus daga mukamin nasa ne a wannan Laraba inda ya ce ya yi haka ne don ya tunkari shari'a da wadanda ya zarga da yin karya a kansa bisa yunkurin bata masa suna.
Akbar dai ya gabatar da kara kan 'yar jarida Priya Ramani, mace ta farko da a ranar Litinin ta zargi ministan da yunkurin lalata. Wasu matan ma dai su 20 sun ce za su ba da shaida kan badalar da ministan ya nemi yi da su.
A watan Yulin 2016 ne dai Akbar ya shiga harkokin gwamnati bayan kwashe shekaru yana aiki a matsayin editan gidan jarida a Kolkata da New Delhi. A baya-bayan nan dai wasu 'yan wasan kwaikwayo a Indiya sun rika kwarmata bayanan wasu na gaba da su a masana'antar fim wadanda ke badala da su.