SiyasaLatin Amurka
Mexico za ta sami mace shugabar kasa
September 7, 2023Talla
Jam'iyya mai mulki ta tsayar da wata wadda ta taba rike mukamin magajin garin birnin Mexico Claudia Sheinbaum a matsayin yar takararta a zaben da za a yi a ranar 2 ga watan Juni.
Sheinbaum dai tana da kusanci da shugaban kasar Andres Manuel Lopez Obrador wanda ba a amince ya sake tsayawa takara ba bayan wa'aadin shekaru shida a karagar mulkin
A makon da ya gabata kawancen Jam'iyyun adawa suka tsayar da Sanata kuma kwararriyar Inginiyar Kwamfuta Xochitl Galvez a matsayin wacce za ta yi musu takarar shugabar kasa.