Mexico ta yi watsi da barazanar shugaban kasar Amirka
April 23, 2018Talla
Ya kuma kara da cewa gindaya wasu sharaddai a kan yarjejeniyar kasuwanci marar shinge na arewacin kasar Amirka zalinci ne,ministan ya yi wadannan kalamai ne bayan shugaba Donald Trump na Amirka ya yi wa kasar ta Mexico barazanar amfani da batun hana kwararar bakin haure a matsayin sharadin ci gaba da kasancewa cikin shirin yarjejeniyar kasuwanci marar shinge,in da ya kara da cewar ya zamar wa Mexico tilas ta dauki matakin hana 'yan cirani shiga kasar Amirka.