1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana farautar wadanda suka kai hari gidan rawa

Ramatu Garba Baba
March 9, 2019

Mutum akalla 15 ne suka mutu wasu 7 suka sami rauni a yayin da 'yan bindiga suka bude wuta kan jama'a da ke tsakiyar cashewa a wani gidan rawa da ke jahar Guanajuato a kasar Mexico.

https://p.dw.com/p/3Ej2g
Mexiko Sechs Menschen wurden in Acapulco getötet
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Hernandez

Tuni aka baza jami'an tsaro don farautar wadanda suka kai harin na wannan Asabar. Hoton bidiyon da aka dauko na ginin,  ya nuna yadda 'yan bindigan da aka fi sani da Sunrise da suka kuma yi kaurin suna a fataucin man fetur ne suka kai harin.

Shugaba Lopez Obrador da ya dare mulkin kasar a watan Disambar bara, ya gaji tarin matsaloli na 'yan daba da masu safarar miyagun kwayoyi, sai dai ya sha alwashin ganin bayan wadannan matsalolin bayan da ya sha ranstuwar kama aiki.