Merkel ta fara tattaunawa da jam'iyyu
January 7, 2018Talla
Angela merkel ta bayyana haka ne a taron tattaunawar da aka soma a birnin Berlin tsakanin jam'iyyun siyasar domin yin sulhu don girka sabuwar gwamnati. Sama da watanni uku ke nan da yin zaben 'yan majalisun dokokin a Jamus sai dai har yanzu babu gwamnati. Tun da farko a cikin watan Nuwamba da ya gabata Angela Merkel ta yi kokarin ganin sun cimma yarjejeniya da jam'iyyun siyasa na FDP da masu kare muhali na Greens hakan ya gaggara.