Merkel: "Babu karin haraji saboda baki"
October 12, 2015Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta bayyana cewa bukatar kudi da ake da ita saboda daukar nauyin ayyukan 'yan gudun hijira ba za ta sanya ba a kara haraji kan al'umma. Shugabar ta bayyana haka ne a yayin wata zantawa da ta yi da wata kafar yada labarai. Shugaba Merkel ta bayyana wa gidan jaridar Bild cewa Jamus ta yi sa'a shekaru da dama tattalin arzikin Jamus na da karfi.
Shi kuwa a nasa bangaren mataimakin shugabar gwamnatin ta Jamus Sigmar Gabriel na jam'iyyar SDP bayyana zarginsa ya yi na cewar mambobin jam'iyyar kawancensu daga jam'iyyar shugaba Merkel ta CDU da CSU daga yankin Bavariya basa yin abin da ya dace kan batun na bada tallafi ga 'yan gudun hijira. Ana dai ci gaba da samun mabanbantan ra'ayoyi a tsakanin 'yan siyasar wannan kasa ta Jamus kan batun na karbar baki.