MDD : Taron koli mai tattare da kalubale
September 24, 2024Za a fara fara taron koli na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, taron da shugabannin kasashe da gwamnatocin duniya fiye da 100 za su gabatar da bayanai da jawabai a mambarin majisar don zayyana halin da kasashe da ma duniya ke ciki.
Karin bayani : Shugabannin Sahel sun yi kira ga MDD da ta hukunta Ukraine
Shugaban Amurka Joe Biden zai fara yaye kallabin taron da nasa jawabin, wanda ke zama irinsa na karshe da Biden din zai gabatar a gaban majalisar a matsayinsa na shugaban Amurka.
Ana sa ran jawabin Luiz Inacio Lula da Silva na Brazil da Turc Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya da Mahmdu Abas na yankin Falasdinu haka da kuma Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Karin bayani : MDD ta ce rikici ya raba mutane miliyan 14 da gidajensu a Afirka
Sai dai taron na zuwa ne a yayin da rikice-rikce ke kara yi wa duniya daurin gwarmai inda batutuwan da za su fi daukar hankali sun hada da batun Sudan da Gaza da kuma yakin da Ukraine ke gwabzawa da makwafciyarta Rasha.